Buhari ya jinjina wa jami’an tsaro kan sako ɗaliban Kagara
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina hukumomin tsaro da na leken asirin kasar da kuma gwamnatin jihar Neja kan rawar da suka taka wajen sako daliban Kagara da ƴan bindiga suka sace
A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar bayan sako ɗaliban a ranar Asabar, Shugaba Buhari ya ce: “Muna farin ciki da aka sake su”.
Ya kuma tausaya wa ma’aikata da ɗaliban da iyayensu kan abin da ya same su.
Ya yi gargadin cewa al’umma ba za ta ci gaba da fuskantar waɗannan hare-hare ba sannan ya umarci jami’an tsaro su shiga farautar ƴan bindigar tare da gurfanar da su a gaban shari’a.