Hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta musanta zargin kama hadimin Ganduje a kan harkokin watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai, ba kamar yadda ake ta yamadidi ba.
Biyo bayan satar daliban kwalejin Jangebe a jahar Zamfara ne Salihu ya caccaki lamirin gwamnatin APC, inda yace gwamnatin ta gaza daga sama har kasa wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.
Salihu ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, amma tun bayan nan ba’a sake jin duriyarsa ba, don kuwa bai kwana a gida ba. Hakan yasa yan uwa da abokansa suke tunanin DSS ce ta kama shi saboda wadannan kalamai nasa.
Sai dai a ranar Asabar, 27 ga watan Feburairu ne daraktan hukumar DSS na jahar Kano, Muhammad Alhassan ya bayyana cewa Salihu baya hannunsu, kuma basu san inda yake ba, inji rahoton Daily Nigerian.
“Ba mu gayyaci Salihu ba, balle kuma mu kama shi. Kada ku manta abokinmu ne, saboda yana bamu shawari a kan harkokin tsaro a jahar Kano.” Inji Alhassan.