- Lamarin Tsaro a Arewa: Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya suna Taro a Kaduna…
Ana dai cigaba da gudanar da taro ne Yau 25/02/2021 a Kaduna akan harkar tsaro karkashin Jagorancin kungiyar Gwamnonin jihohin Arewa wadda Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong ke jagoranta, taron yana gudana ne a fadar gwamnatin Jihar Kaduna.
Makasudin taron dai shine tattauna matsalar tsaro a yankin na Arewa taron ya samu halartarcin shugaban majalisar dattawa Senator Ahmed Lawan da Gwamnonin jihohin Arewa Goma Sha Tara Sai Shugaban Maaikatan fadar Shugaban Kasa Ambassador Ibrahim Gambari da kuma mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Babagana Mongunu.
Sauran sun hada da Ministan yada Labarai Alhaji Lai Muhammed da Sufeto janaral na rundunar Yansandan Muhammed Ibrahim Adamu da shugaban hukumar Jami’an tsaron farin kaya Yusuf Bichi.
Suma dai Sarakunan Gargajiya ba’a barsu baya ba sun halarci taron karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad na Biyu Sai Sarkin Katsina Alh. Abdulmumin Kabir Usman da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero dama Sarkin Zazzau.
Anyi taron ne domin samun mahita ta dindindin akan harkokin tsaro da suka tabarbare, musamman matsalar garkuwa da mutane, hare hare da sauran su, hade da samar wa da matasa aikin yi.
Taron dai zai kwashe kwana biyu ana gudanar dashi inda ake sa ran kammala shi a gobe, Juma’a Idan Allah ya kaimu.