Hon. Jamilu Yahaya Kankara wanda aka fi sani da Hon J. Man (Na Matasa) a karshe ya amince ya shiga takarar zaben 2023 karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.
Hon J. Man ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar dan majalisa mai wakiltar mazabar Kankara a majalisar dokokin jihar Katsina a wata tattaunawa da ya yi da wakilin Daily Episode.
A cewarsa, an yanke wannan shawarar ne bayan tuntuba mai yawa, kiraye-kiraye da dama, da kuma amincewa daga kungiyoyi masu zaman kansu, daidaikun jama’a, kungiyoyin dalibai, da kungiyoyin goyon bayan siyasa kan burinsa.
Idan dai za a iya tunawa J.man ya tsaya takarar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kankara a zaben 2019, wanda Hon. Mamman Sani wanda ya kasance tsohon Shugaban karamar Humar Kankara kuma tsohon dan majalisar wakilai ne yayi nasara da kuri’u goma sha daya kachal.
Sai dai ya kara tabbatar wa da masu zabe, wakilan jam’iyya, da masu ruwa da tsaki a kan aniyarsa ta bayar da tasa gudunmawar ga ci gaban Kankara, Jihar Katsina, da Nijeriya baki daya.
Zan ba da wakilci mai kyau kuma mai ma’ana ta hanyar tabbatar da yin magana da warware matsalolin da aka gano a Kankara a cikin iyawa ta.
Domin yakar tabarbarewar rashin tsaro da rashin aikin yi, zan kuma bullo da tsare-tsare don rage radadin talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa, mata, da sauran jama’a.
Hon J.man Ya kara da cewa Na shirya kuma na dauki nauyin shirye-shirye ga dalibai, kuma insha Allahu zan yi aiki idan aka zabeni a matakin Jamiyya PDP kuma aka ayyanani wanda ya lashe zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta zata shirya. domin ilimi shi ne hanya mafi dacewa wajen magance wannan matsalar rashin tsaro da ta addabi kasarmu.
Da yake godewa jam’iyyar PDP bisa damammaki da ta ba shi, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi rajistar masu kada kuri’a da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ke yi domin zaben yan takarar da suka dace domin ceto Najeriya daga halin da take ciki a zaben 2023