Jami’an ƴan sanda a Jihar Kaduna sun tabbatar da kama mutane 13 da ake zargi da hannu a kisan wani jami’in sojan ruwa, LT Commodore M. Buba, a yankin Kawo da ke birnin Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Mansir Hassan, ya bayyana cewa rundunar ta kai samame a yankin Kawo, inda ta kama mutane 13 da makamai masu hadari a hannunsu.
Rahoton ya nuna cewa marigayin jami’in soja wanda ke karatu a matsayin ɗalibi mai matsayi a Makarantar Horas da Jami’an Tsaro ta Hadin Gwiwa da ke Jaji, ya gamu da ajalinsa ne da safiyar Lahadi, da misalin ƙarfe 5:20 na safe, a kusa da gadar sama ta Kawo.
A cewar jami’an tsaro, lamarin ya faru ne yayin da sojan ke kan hanyarsa daga Jaji zuwa cikin birnin Kaduna, sai tayar motarsa ta fashe. Yayin da yake ƙoƙarin canja taya, wani mutum da ba a san ko wanene ba ya taso masa da bukatar ya miƙa wayarsa ta hannu.
“Da jami’in ya ƙi, yana tambayar dalilin hakan, sai mutumin nan ya ciro wuka ya soka masa a ƙirji,” in ji sanarwar ƴan sanda.
Sai dai, kafin mutumin ya tsere daga wurin, mutane da ke kusa da wajen sun tare shi, suka kuma yi masa dukan kawo wuka, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
An garzaya da jami’in sojan zuwa asibitin Manaal domin ceto rayuwarsa, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa tun kafin a isa. Daga nan ne aka mayar da gawarsa zuwa Asibitin 44 Army Reference Hospital da ke Kaduna.
Rundunar ƴan sanda ta ce bincike yana ci gaba domin gano ƙarin bayani kan lamarin, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu cikin wannan mummunan aiki.
KU BIYO MU A FACEBOOK