Yayin da ruwan sama ke sauka a sassan Najeriya, manoma sukan fara shirin noma da farin ciki, amma a Karamar Hukumar Kankara da ke kudancin Jihar Katsina, fargaba da tsoro sun mamaye zukatan al’umma.
‘yan bindiga sun kai hari, inda suka kashe fiye da manoma 30 a ƙauyuka daban-daban da suka haɗa da: Yar Goje, Dan Marke, Burdigau, Gidan Daudu, Gidan Damo, Marmara, Unguwar Tofa, Barebari, Unguwar Gambo, Kwakware, da Santa Dan Geda.
Harin ya auku ne a ranar 16 ga Yuni, 2025. Wasu sun tsira da raunuka sakamakon harbin bindiga, yayin da akayi garkuwa da wasu da dama, kamar yadda wani ganau mai suna Malam Isa (ba sunansa na gaskiya ba) ya shaida wa Jaridar Daily Episode.
A hirarsa da wakilinmu, Malam Isa ya ba da labarin yadda aka harbe abokinsa bayan sun kammala aikin gona.
“Ina zuwa daga nesa don na huta tare da abokina. Cikin sauri na ji harbin bindiga. Na san mun shiga haɗari. Kafin in yi wani yunkuri, tuni suka kewaye Aminu Gurgu. Wasu daga cikinsu suna masa tambayoyi amma daga inda nake a boye, ban iya fahimtar me suke fada masa saboda ina nesa ga kuma fargaba,” in ji Isa.
“Abin bakin ciki, na ga yadda ɗaya daga cikinsu ya harbe Aminu a kai, sannan ya caje aljihunsa, ya sace wayarsa da kuɗinsa, sannan suka nufi kauyen Marmara inda suka kashe wasu ‘yan’uwa guda biyu, Alhaji Isuhu da wani ɗan’uwansa da na manta sunansa ba,” in ji Isa cikin hawaye.
Wani mazaunin kauyen Burdigau, Malam Yakubu Birdigau, ya bayyana wa Daily Episode cewa ‘yan bindigar sun fito ne daga dajin da ke kusa da yankin. Ya ce, “Ko wace shekara ko da zarar ruwan sama ya fara sauka, sai sun kawo hari, su kuma tilasta wasu al’umma su biya haraji kafin su samu damar noma gonakin su.”
Sai dai a wannan karon, lamarin ya fi muni. “Fiye da mutane 30 aka kashe a harin. Hatta gawar mutumin da muka rasa tun farko, sai bayan kwana uku aka samu gawarsa a daji ta kumbura ta fara wari,” in ji Malam Yakubu.
Ya kara da cewa, “Lokacin da aka fara harbin, mun yi zaton jami’an tsaro za su zo ceton mu, amma babu wani ƙoƙari na kawo ɗauki. haka suka gama kashe mutane cikin kwanciyar hankali, babu wanda ya hana ko ya kawo mana agaji.”
“Mun kirga mutane sama da 30 da suka mutu a ƙauyukan Yar Goje, Dan Marke, Burdigau, Gidan Daudu, Gidan Damo, Marmara, Unguwar Tofa, Barebari, Unguwar Gambo, Kwakware da Santa Dan Geda a rana ɗaya. Game da adadin waɗanda aka sace, ba zan iya tabbatar da yawansu ba. Abin takaici ne, gwamnatin ba ta da karfi da zai hana waɗannan hare-hare,” in ji shi.
Rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da cikakken bayani ba kan harin, duk da alkawarin da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya bayar na cewa zai turu mana bayanan bayan da muka tambayeshi.
KU BIYO MU A FACEBOOK