">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Thursday, October 16, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

’Yan Fada Sun Kange Buhari Daga Masu Fadar Gaskiya —Dalung

by Maryam Umar Said
August 13, 2021
in Sport Stories
0
’Yan Fada Sun Kange Buhari Daga Masu Fadar Gaskiya —Dalung
Share on FacebookShare on Twitter
">

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung ya koka kan abin da ya kira wadansu makusantan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suna kange shi daga masu kokarin dora shi a turba tagari da yi wa ’yan kasa hidima.

Solomon Dalung ya ce na kusa da Shugaban Kasar sukan ba da uzuri na bogi cewa akwai annobar COVID-19 don haka ba za a iya ganawa da shi ba.

Ya bayyana haka ne yayin hira da kafar labarai ta Legit a ranar Litinin da ta gabata.

Da aka tambaye shi game da aikin da na kusa da Shugaban suke yi don ganin sun wanke Najeriya daga kunya a idon duniya, musamman a fannin tsaro, Mista Dalung ya ce, “Yana yiwuwa wadanda suke kange Shugaban Kasa yanzu ba sa son a ba shi wata shawara a kan abin da yake faruwa.

RelatedPosts

Gobarar Tankar Fetur Ta Yi Ajalin Mutane da Dama a Neja

Iyalan Waɗanda Harin Sojoji ya Shafa a Zamfara Sun Nemi Diyya da Tallafi

Kananan Hukumomi Za Su Fara Karɓar Kuɗaɗensu Kai Tsaye – Fadar Shugaban Ƙasa

Kano Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Rahoton Cutar Murar Tsuntsaye

“Ke nan suna da niyyar su ba shi kunya da rushe kyakkyawar manufar da yake da ita, shi ya sa suka hanawa tare da kange mutane zuwa jikinsa.

“Ai yana zuwa taro, yana karbar baki, muna ganin yana karbar mutane, wadannan mutanen ba su da COVID-19 ne? Ko sai mu da za mu zo mu gan shi ne za mu cutar da shi?”

Game da zargin Shugaba Buhari da gazawa wajen magance matsalar tsaro, Mista Dalung ya ce Shugaban bai gaza ba.

“Ina ganin kamar matsalar tsaro da aka shiga, wadda ’yan Najeriya suke fama da ita a kowace rana, da zargin Shugaban Kasa cewa ya gaza, ina ganin ba lallai ya gaza ba ne.

“Amma wane irin bayani yake zuwa gare shi? Shin abubuwan da suke faruwa yana jin su kamar yadda suke faruwa?

“A nawa tunanin Shugaban Kasa ya shiga halin da mutane wadanda za su ba shi shawara mai kyau sai dai su je kusa da shi su kadai.

">

“Wannan a yi addu’a ga Allah, Allah Ya taimaki Shugaban Kasa ya fita daga cikin wannan hali,” inji shi.

">

DAILY EPISODE HAUSA

KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER

Source: Dailytrust
Maryam Umar Said

Maryam Umar Said

Related Posts

Gobarar Tankar Fetur

Gobarar Tankar Fetur Ta Yi Ajalin Mutane da Dama a Neja

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Mutane da dama, ciki har da wata mai juna biyu, sun rasu yayin da gobara ta tashi lokacin da suke...

harin jiragen Sojin

Iyalan Waɗanda Harin Sojoji ya Shafa a Zamfara Sun Nemi Diyya da Tallafi

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Iyalan waɗanda harin jiragen Sojin saman Najeriya ya rutsa da su a Zamfara sun nemi gwamnati ta biya su diyya...

Asusun Bai Ɗaya

Kananan Hukumomi Za Su Fara Karɓar Kuɗaɗensu Kai Tsaye – Fadar Shugaban Ƙasa

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa, daga ƙarshen watan Janairu, dukkan kananan hukumomi a Najeriya za su fara karɓar...

Murar Tsuntsaye

Kano Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Rahoton Cutar Murar Tsuntsaye

by Abubakar Ismail kankara
January 17, 2025
0

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali tare da kai rahoton duk...

Biden da Netanyahu sun tattauna kan tsagaita wuta a Gaza

Biden da Netanyahu sun tattauna kan tsagaita wuta a Gaza

by Abubakar Ismail kankara
January 13, 2025
0

Shugaban Amurka, Joe Biden da Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu sun tattauna ta waya a daidai lokacin da ake ci gaba...

rikicin masarautar Kano

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Umarci Sake Sauraron Shari’ar Rikicin Masarautar Kano

by Abubakar Ismail kankara
January 10, 2025
0

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta bayar da umarnin sake sauraron shari’ar rikicin masarautar Kano da ya haɗa da...

Next Post
Sojoji Na Iya Bakin Kokarinsu Wajen Kawo Karshen Ýan Bindiga – Jihar Neja

Sojoji Na Iya Bakin Kokarinsu Wajen Kawo Karshen Ýan Bindiga - Jihar Neja

Tare Za Mu Cimma Nasara – Matasa

Tare Za Mu Cimma Nasara - Matasa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In