Ƴan bindiga sun dauke matar tsohon dagacin kauyen Kofa na karamar hukumar Kusada, a jihar Katsina.
Alhaji Rabe Bello Kofa, ya rasa ransa ne a ranar talata inda kuma akayi jana’izar sa.
Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun far wa kauyen ne da sanyin safiyar Laraba.
Inda suka nufi gidan dagacin kauyen da ya rasu ranar Talata suka dauke wasu daga cikin iyalansa da ke zaman makoki, ciki harda matarsa.
“Maharan sun kutsa gidan marigayin inda suka yi awon gaba da wasu iyalansa biyar ciki har da mai dakinsa, amma daga bisani sun saki sauran hudun suka yi garkuwa da matar,” in ji shi.
Marigayin Alhaji Rabe Bello Kofa, dagacin kofa da ya rasu dan uwan tsohon shugaban kakakin majalisar Katsina ne.
Da aka tuntube kakakin ƴan sanda Katsina, SP Gambo Isah ya ce zai tuntubi jami’in da ke kula da yankin.