‘Yan bindiga sun kai hari Makarantar horas da Sojoji ta Nigeria Defence Academy, NDA, da ke garin Kaduna
A yadda rahotanni suka zo mana ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda daya yayin harin da suka kai misalin qarfe 1 na daren Litinin.
Mai magana da yawun Makarantar Sojojin, Manjo Bashir Muhammad Jajira, ya tabbatar da kai harin.
Ya ce ‘yan bindigar sun shiga bangaren gidaje na Makarantar inda suka kai hari, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’ansu biyu sannan aka sace guda daya.
Manjo bashir ya tabbatar da cewa, mazauna barikin NDA da ‘yan makarantar horas da sojoji suna cikin koshin lafiya a Makarantar.
Muna tabbatar wa jama’a cewa za a kamo wadannan ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba nan gaba kadan, sannan a ceto jami’in da aka sace, kamar yadda ya fada.
Ya kara da cewa hukumomin Makarantar da hadin gwiwar Runduna ta Daya ta Sojin Kasan Najerriya da Rundunar Horas da Sojin Sama da ma sauran jami’an tsaro da ke Kaduna, sun soma bin bayan ‘yan bindigar da zummar far musu da kuma ceto wanda aka sace.
Al’amarin ya girgiza ýan Najeriya, inda suke cikin rudanin ganin cewa wadanda zasu ba su kariya su ma ba su tsiraba.