A karo na biyu, mahara sun kai hari kan wasu al’umomi a masarautar Miango ta jihar Filato ranar Litinin wanda ya janyo rasa rayuka da asarar dukiya mai dumbin yawa.
Tun ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga suka fara afka wa kananan hukumomin Bassa da Riyom na jihar, inda suka kona daruruwan gidajensu, baya ga barnata amfanin gona a yankin.
Rahotanni daga kafofin yada labarai a Najeriya na cewa kimanin gawa 43 aka gano zuwa safiyar yau Talata a wasu kauyukan da ke masarautar Irigwe da ke karamar hukumar Miango.
Shugabannin masarautar Iregwe, wadanda hare-haren suka fi shafa sun koka kan yadda jami’an tsaro suka kyale maharan su ci gaba da kai hare-haren da suka shafe kwana uku suna ka wa a yankin.
Prince Robert Irigwe Ashidodo, shugaban kungiyar raya masarautar Iregwe ya shaida wa BBC Hausa cewa jami’an tsaron da aka tura yankin sun ki daukar mataki kan maharan duk da cewa mazauna kauyukan sun sanar da su halin da suke ciki.
Mista Dan Manjang wanda shi ne kwamishinan yaɗa labarai na jihar ta Filato, ya faɗa wa BBC Hausa cewa duk da cewa tsaron rayuka ya rataya a wuyansu amma harkar tsaro ta dukkan jama’ar gari ce.
Duk ƙoƙarin da BBC ta yi na ji daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Filato bai yi nasara ba saboda yana mai bayar da uzurin cewa yana asibiti wajen duba maras lafiya.
A ranar Litinin Auta Danjuma, wani jigo a masarautar Irigwe, ya shaida wa BBC cewa suna zargin Fulani makiyaya da kai hare-haren. Sai dai Muhammadu Nura Abdullahi, shugaban kungiyar Mi Yetti Allah ta Fulani makiyaya a jihar Filato, ya musanta zargin.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER