Gwamnatin tarayya ta saba alkawarin da ta dauka, wanda hakan ya janyo kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, shawarar komawa yajin aiki.
Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa, za su koma yajin aikin ne sanadiyyar rashin cika alqawarin da gwamnatin ta yi bayan cimma matsaya da sukayi sannan kuma taki amsa kiraye kirayensu.
Shugaban kungiyar ya tabbatar da cewa sun baiwa gwamnatin zuwa Talata ne 31 ga watan Agusta akan ta cika alkawuran da suka dauka ko kuma su koma yajin aiki.