Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin tsaron kasarnan, ana sa ran tattaunawar ne a kan yanayin tsaron kasar.
Mashawarcin Shugaban Kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.
Rahotanni na bayyana cewa wadanda suka halarci taron sun hada da ministan tsaro, manjo janar Baashir Salihi Magashi, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ministan harkokin qasashen waje, Geaffery Onyeama, ministan shari’a Abubakar Malami da mai kula da ayyukan ýan sanda Mai gari Dingyadi.
Babban hafsan sojoji Lucky Irabour da sufeton ýan sanda Usman Alkali Baba da kuma sauran shuwagabannin tsaro ne zasu yiwa shugaba Buhari bayani kan yanayin tsaron kasarnan a halin da ake ciki yanzu.