A zaman da ya wakana a jiya Talata a fadar shugaban kasa kan yanayin tsaron kasar nan, shugaba Buhari ya bukaci shugabannin tsaron da su samar da sabbin hanyoyi da dabarun da za su magance matsalolin tsaron kasar nan.
Hakan ya biyo bayan bayanin da shugabannin tsaron sukayi kan yanayin tsaron kasar.
Bayan kammala ganawar ne sufeton ýan sanda Usman Alkali Baba ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya bukaci a kirkiro sabbin dabarun ne sakamakon yawan sace-sace da kashe-kashen mutane da ya addabi yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya.
Sufeton ya ce, shugaba Buhari ya umarci shugabannin tsaron da su kara jajircewa wajen kawo zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.