Shugaba kuma mawallafin jaridar Blueprint, Muhammad Idris, ya bayyana cewa sasanci da ýan ta’adda da kuma samun daidaiton ra’ayi tsakanin gwamnoni wajen tsaro shine kadai hanyar da za a samu zaman lafiya a yankunan da ta’addancin ya addaba.
Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya halarta wanda Nigerian Institute of Public Relations (NIPR) ta shirya.
Ya goyi bayan Gwamnatin Kaduna a kan kin tattaunawa ko biyan kudin fansa ga ‘yan ta’addan domin a cewarsa be kamata ace suna cin ribar laifukan da suke aikatawaba.
Amma yana da muhimmanci a samar da wata hanya da zata bada damar sanin halin da ýan ta’addan ke ciki, wanda hakan zai bada damar samun mafita a harkokin tsaro.
Ya qara da cewa, ya zama dole ga al’umma su samar da hadin kai tsakaninsu domin kawo karshen wannan halin da ake ciki.
A zaman taron Dr. Shu’aibu Shehu Aliyu ya qara da cewa rashin samun daidaito tsakanin gwamnonin wajen shawo kan matsalar tsaro shine babban dalilin da ya sa aiyukan ta’addancin ke kara habaka a arewacin Kasar nan.
Kamar yadda ya ce, wasu Gwamnonin na neman sasanci da tattaunawa da ýan ta’adda, wasu kuma basu bada kofar hakan ba, a yayinda kuma samun daidaiton matakan ne zai kawo zaman lafiya a yankunan.
Ya kara da cewa bayanai sun bayyana cewa, masu satar shanu na fitar da shanu zuwa kasashen kewaye kamar su Mali, Ivory coast, Chad da sauransu a madadin makamai, wanda rashin daukar mataki a kan hakan zai wanzar da ci gaban ta’addanci.
A kwana kwanan nan Dr. Ahmad Sheikh Gumi yayi magana makamanciyar wan nan.