Sabuwar dokar man fetur doka ce da aka dade ana sa ran a qaddamar da ita tun lokacin mulkin tsohon shugaban qasa Olusegun Obasanjo inda ya aike da dokar zuwa majalisar dattawa ta qasa a Afrilun shekarar 2002, haka shuwagabannin qasar da suka biyo baya ma, amma dokar bata samu sahalewar majalisar ba sai a shekarar 2018, inda a Augustan 2021 ne shugaba Muhammadu Buhari ya samu damar rattabawa dokar hannu.
Hukumar da ke kula da farashin mai a Najeriya ta bayyana cewa akwai matakai da gwamnati ke ɗauka ta yadda ba za a samu hauhawar farashin mai ba sakamakon sauye-sauyen da sabuwar dokar inganta harkar ta kawo a ƙasar.
Tun da gwamnatin APC a Najeriya ta sanar da matakin rusa babban kamfanin mai na ƙasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a yi wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur, ƴan ƙasar ke bayyana fargaba ga yiyuwar tsadar farashin man fetur.
Babban jami’in hulɗa da jama`a na hukumar PPPRA da ke kula da farashin mai a Najeriya Kimchi Apollos, a hirarsa da BBC ya kawar da fargabar da wasu ke yi cewa za a samu karin farashin mai.
Ya ce gwamnati na tattaunawa da ɓangaren ƙungiyoyin kwadago da nufin ɗaukar matakan da za su taimaka wajen ganin farashin man bai jefa ƴan Najeriya cikin wahala ba.