A yayin zaman da babbar kotun Addinin musulunci da ke kofar kudu tayi, qarqashin jagorancin Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola, a ranar Alhamis da misalin qarfe 9:20 na safe, inda aka gabatar da sabbin tuhumomi guda hudu ga sheikh Abduljabbar.
Zaman ya kaya kamar haka:
Tuhuma ta farko ita ce: “Ranar 10 ga watan 8 a shekara ta 2018 Abduljabbar a unguwar Sani Mainagge a karatunka na Jauful Fara inda ka yi wa Annabi SAW kage na cewar a Hadisi na 1365 da na 1358 na sahihi Muslim cewa Annabi SAW fyade ya yi wa Nana Aisha, wanda hakan ya saba wa 382 (b) kundin tsarin shari’ar Musulunci ta 2000.”
Shiru ne ya biyo bayan tambayar inda Abduljabbar bai amsa ba, hakan ya sa kotu ta tambaye shi yaren da yake ji, amma nan ma bai ce komai ba.
Kotu ta ci gaba da yi masa tambaya har sau uku amma bata samu kowanne amsa daga Abduljabbar ba.
Tuhuma ta biyu: “Ranar 10 ga watan 8 2018, a karatunka na Jauful fara ka yi amfani da kalaman ɓatanci inda ka yiwa Annabi (SAW) kage kan aurensa da Ummu Safiya, ka ce Sahihi Muslim ya ce Annabi ya kwace wa wani mutum matarsa 1365, wanda hakan cin zarafi ne, laifi ne da ya saba wa sashe na 382(b)”
A wannan karon ma Abduljabbar shiru ya yi.
Alkali ya sake tambaya: “Shin ka yarda ka aikata laifi ko ba ka yarda ba?”
Abduljabbar ya yi shiru bai ce komai ba.
Tuhuma ta uku: “A ranar 10 ga watan 8 ta shekarar 2019, a darasinka na 93 ka yi amfani da kalaman ɓatanci cewar dole manzon Allah ya yi wa matarsa Safiyya ya aureta, wanda babu wannan hadisi kai ka kirkire shi. Kuma hakan ya saɓa wa sashe na 382 (b) na kudin tsarin Shari’ar Musulunci na Kano na 2000.”
Kan wannan tuhumar ma dai Abduljabbar bai ce komai ba.
Tuhuma ta hudu: “A darasinka na 90 da na 98 na karatun Jauful fara ka kaga wa Annabi laifin zina, inda ka ce wata mata ta nemi Annabi ya biya mata bukatarta, kuma ka ce ya yi hakan, wannan ya saɓa wa sashe na 382 na kundin hukunta laifuffuka na shari’ar Musulunci na 2000 ta jihar Kano.
Alkali Sarki Yola ya sake tambayar Abduljabbar ko ya yarda da aikata laifin amma ya yi shiru bai ce uffan ba.
Sabbin zarge-zarge guda hudun da aka karanta wa Sheikh Abduljabbar dai sun shafi zargin yin batanci da kuma cin zarafin Annabi Muhammad (SAW) ne yayin karatuttukansa na Jauful-Fara, inda kuma yaqi cewa komai.
Sai dai a cewar masu kara ya saba da tanade-tanaden sashe na 382(b) na Kundin Dokokin Shari’ar Musulunci na Jihar Kano na 2000.
Lauyan da ke kare Abduljabbar, Barista Saleh M. Bakaro ya shaida wa kotun cewa masu shigar da kara ba su da damar janye zarge-zargensu na farko domin su canza su da wasu sabbi ana tsaka da shari’ar.
Sai dai amsar alkalin ta kore qorafinsu in da ya ce suna da ikon yin hakan dogaro da sashe 390 (i) na kundin dokokin ACGL na 2015.
Alkali ya bada umarnin bincikar lafiyar kwakwalwa da kunnen Sheikh Abduljabbar saboda rashin amsawa kotu tambayoyin da ta yi masa.
Masu Kare wanda ake tuhuma sun bukaci daukaka kara, inda Alkali ya umarci a bai wa lauyoyin wanda ake kara kwafin shari’ar domin daukaka karar da suke bukata.
Ya kuma shaida cewar za a cigaba da sauraron karar du da haka.
Daga nan ya ɗage zaman shari’ar zuwa mako biyu masu zuwa, inda za a dawo kotu ranar 16 ga watan Satumbar 2021 domin ci gaba da shari’ar.