Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar Nuhu Aliyu, tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a majalisar dattawa, ya rasu. Aliyu wanda ya kasance mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda mai ritaya ya rasu a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 79 a duniya.
Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da mutuwar tsohon dan majalisar. Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana rasuwar Aliyu a matsayin babban rashi ga jihar Neja da ƙasa baki ɗaya.
”Kishin kasa da kyakkyawar riko wajen gudanar da ayyukan majalisa game da jin dadin jama’a da marigayi Sanata Nuhu Aliyu ya nuna sun cancanci ayi koyi da su. “Amma dole ne mu rarrashi zuciyarmu cewa daga Allah muke kuma gare Shi duk za mu koma. Babu wanda zai rayu fiye da lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya diban masa.”
Marigayi dan siyasar ya kasance jigon jam’iyyar PDP na farko a jihar Neja kafin a zabe shi a majalisar dattijai a 1999 sannan aka sake zabar shi kan wannan matsayi a 2003 da 2007.
Tuni dai aka yi jana’izar shi kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada. Allah Muke Roko Ya Jiƙansa Ya Gafarta Mishi Allahumma Amin.