Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce Najeriya ta na mataki na hudu cikin jerin kasashen da suke yaki da cutar korona.
Wakilin WHO a Najeriya Dr. Walter Mulombo ne ya bayyana hakan a wajen karbar rigakafin korona sumfurin Johnson and Johnson kimanin 177,600 da suka karaso Abuja.
A kalla rigakafin miliyan 1 da dubu 173, da 132 ne suka fara isowa, cikin rigakafi miliyan 8 da dubu dari 8 da bankin hada hadar kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika ya fara aikowa da su zuwa qasar nan.
A cewar WHO wannan ne ya baiwa Najeriya damar zuwa mataki na 4 na kasashen da suka fi yaqi da cutar korona a fadin duniya.