Canja shekar da wasu daga cikin ýan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagle sukayi bazai kawo naqasu a wasan da kungiyar zata buga ba da Cape Varde a yau Talata.
Kaftin din kwallon kafa ta kasa Ahmad Musa ya tabbatar da cewar sunyi rashin ýan wasa wadanda suke taimakawa kungiyar, amma suna da wadanda zasu maye gurbin su.
Kaftin din ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai.
Najeriya zata buga wannan wasan ne domin neman tikitin buga kofin duniya wanda kasar Qatar zata karbi bakunci a 2022.
A wasan farko da kungiyar ta Super Eagle ta buga da Liberia a nan gida Najeriya tayi nasara da ci 2-0.