">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Wednesday, October 15, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Manyan APC Da PDP Sun Mayarwa Farfesa Jega Martani

by Maryam Umar Said
August 4, 2021
in Music
0
Manyan APC Da PDP Sun Mayarwa Farfesa Jega Martani
Share on FacebookShare on Twitter
">

Jam’iyyar APC mai mulki da PDP mai hamayya sun mayar wa tsohon shugaban hukumar zaɓe (INEC) na ƙasar martani game da kalamansa da ya yi cewa sun gaza kuma “kar ‘yan Najeriya su sake zaɓen su”.

Cikin wata hira da BBC Hausa ranar Litinin, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa “APC da PDP sun yi [mulki] duk mun gani, ba gyara suke nufi ba”, yana mai cewa ya shiga jam’iyyar PRP.

“Idan ka dubi yaƙi da cin hanci da rashawar nan, duk mutanen da ake cewa ɓarayi ne za a hukunta su saboda sun yi sata a karkashin PDP, yanzu sun lallaɓa sun koma APC, kuma shiru kake ji,” in ji shi.

A cewarsa: “Shi ya sa mu muke ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a samar da wata dirka da duk mutumin kirki zai koma cikinta, domin bayar da tasa gudunmawar wajen kawo gyara a Najeriya.

RelatedPosts

Gurbatattun ‘Yan Siyasa Ke Haddasa Rashin Tsaro Da Kabilanci A Nijeriya – Jigon Jam’iyyar APC

Yanzu Yanzu: Dr Surajo Yakubu Batagarawa Ya Sauya Sheka Daka PRP Zuwa APC

APC Zatayi Shekara 32 Tana Mulki: Shiga Hurumin Ubangiji Ne – Hadimin Gwamna Masari Sabo Musa

APC ba Ta isa Ta kwashe shekara 36 Tana Mulki ba – PDP

Dukkan APC da PDP babu wadda ta yarda da maganar tsohon shugaban INEC ɗin cewa ta gaza wajen kyautata rayuwar `yan Najeriya ballantana a ce kar a zabe ta a nan gaba.

Martanin PDP

Babbar jam`iyyar hamayya ta PDP ta yi iƙirarin cewa ta cimma nasarori masu ɗimbin yawa a lokacin da APC ta ƙwace mulki daga hannunta, saɓanin matsain rayuwar da `yan kasar ke fama da shi a halin da ake ciki.

PDP ta ce ba ta musanta cewa APC ta gaza ba amma idan har za a yi ƙwaƙwa, to tsohon shugaban hukumar zaben ma da nasa laifin, saboda da shi aka yi uwa da makarbiya wajen bai wa APC nasara a lokacin da ta yi wa PDP kaye.

Mista Kola Olagbondiyan, shi ne Sakataren Yaɗa labaran PDP, kuma ya faɗa wa BBC Hausa cewa abin takaici ne yadda Jega ya nuna “rashin fahimtarsa a fili” a matsayinsa na farfesan kimiyyar siyasa.

“Ya kamata a tunasar da Farfesa Jega yadda PDP ta haɓaka tattalin arzikin Najeriya, ta biya tulin bashin da ake bin ta…har ma tattalin arzikinta ya zama ɗya daga cikin mafiya haɓaka cikin sauri kuma cibiyar zuba jari mafi girma a Afirka.

">

“Amma sai APC ta zo ta lalata shi sannan ta mayar da ƙasarmu babban birnin talauci na duniya da kuma cin bashi a cikin shekara shida.”

Martanin APC

Ita ma jam`iyyar APC a nata martanin, ta yi ikirarin cewa ta gaji tarin kura-kurai da ta zargi gwamnatin PDP da bar mata, tana mai cewa abubuwan da Shugaba Buhari ya cimma “zarta na PDP”.

Ta yi ikirarin cewa ta gaji tarin kura-kurai da ta zargi gwamnatin PDP ta bar mata, wadanda take fadi-tashin gyarawa,

">

Kazalika, ta yi wa Farfesa Jega ba’a tana mai cewa watakila yana jiran ta yi masa tayi ne tun da ya shiga siyasa.

“Idan jam’iyyar APC ya ke so ya shigo to sai ya zo ofis ɗinmu ya karɓi takardu ya karanta domin ya fahimta sosai ya shigo,” in ji Daraktan Yaɗa Labaran APC na Ƙasa, Mallam Salisu Na`inna Danbatta.

Sai dai ya ce Farfesa Jega ya yi gaskiya kan abubuwan da ya faɗa a kan PDP.

DAILY EPISODE HAUSA

KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER

Maryam Umar Said

Maryam Umar Said

Related Posts

Gurbatattun ‘Yan Siyasa Ke Haddasa Rashin Tsaro Da Kabilanci A Nijeriya – Jigon Jam’iyyar APC

Gurbatattun ‘Yan Siyasa Ke Haddasa Rashin Tsaro Da Kabilanci A Nijeriya – Jigon Jam’iyyar APC

by Abubakar Ismail kankara
April 12, 2021
0

Wani jigon jam’iyyar APC ya bayyana cewa, ba za a taba samun daidaituwa a Nijeriya har sai ‘yan siyasa sun...

Yanzu Yanzu: Dr Surajo Yakubu Batagarawa Ya Sauya Sheka Daka PRP Zuwa APC

Yanzu Yanzu: Dr Surajo Yakubu Batagarawa Ya Sauya Sheka Daka PRP Zuwa APC

by Abubakar Ismail kankara
April 4, 2021
0

UWAR JAM'IYYAR APC TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA AMSHI DR SURAJO YAKUBU BATAGARAWA YAU LAHADI 4/4/2021,,, ________________ Uwar Jam'iyyar Apc...

APC Zatayi Shekara 32 Tana Mulki: Shiga Hurumin Ubangiji Ne – Hadimin Gwamna Masari Sabo Musa

APC Zatayi Shekara 32 Tana Mulki: Shiga Hurumin Ubangiji Ne – Hadimin Gwamna Masari Sabo Musa

by Abubakar Ismail kankara
March 31, 2021
0

Hadimin gwanan yayi wannan bayani ne a wata hira da akayi dashi a yau laraba 31 ga watan mayu shekarar...

APC ba Ta isa Ta kwashe shekara 36 Tana Mulki ba – PDP

by Abubakar Ismail kankara
March 24, 2021
0

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi raddi kan kalaman da abokiyar hamayyarta APC mai mulkin kasar ta yi...

APC Tasha Alwashin Yin Shekara 32 Kan Karagar Mulki Don Inganta Rayuwar Al’umma’

APC Tasha Alwashin Yin Shekara 32 Kan Karagar Mulki Don Inganta Rayuwar Al’umma’

by Abubakar Ismail kankara
March 24, 2021
0

Shugaban Kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu ta tsara yadda za ta ci gaba da...

A shirye nake na fice daga jam’iyar APC matukar masu yi min zagon kasa ba su hankalta ba__Ahmad Bola Tunibu ga APC.

A shirye nake na fice daga jam’iyar APC matukar masu yi min zagon kasa ba su hankalta ba__Ahmad Bola Tunibu ga APC.

by Abubakar Ismail kankara
March 6, 2021
0

Biyo bayan tambarin bincike da hukumar EFCC ta dasa akan jigo a jam’iyar APC, Ahmad Bola Tunibu ya yi magana...

Next Post
Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Aminu Ala Rasuwa

Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Aminu Ala Rasuwa

Jamhuriyar Nijar Ta Cika Shekara 61 Da Samun ’Yanci

Jamhuriyar Nijar Ta Cika Shekara 61 Da Samun ’Yanci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In