Babbar kotun tarayya dake Fatakwal na jihar Rivers, ta dakatar da hukumar tattara kudin haraji ta kasa Najeriya (FIRS) karbar harajin sayen kayayyaki na (VAT).
Hakan ya sa hukumar ta daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun ta yanke.
Daraktan sadarwa tare da hulda da jama’a na hukumar, Abdullahi Isma’ila Ahmed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Inda hukumar take neman a dakatar da hukuncin, har sai kotu ta saurari karar da ta daukaka.
Du da haka hukumar na shawartar al’umma da su ci gaba da biyan kudaden harajin har sai kotun daukaka kara ta warware lamarin.