Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da sanarwar cewar bata da wani quduri na rufe layukan waya a jihar, hakan jita-jita ce kawai mara tushe.
Mai baiwa Gwamnan Kaduna shawara Muyiwa Adekeyi ya bayyana cewa “Gwamnatin Kaduna bata da wani nufi na dakile kafar sadarwa, kuma bata tunanin daukar matakin hakan a halin yanzu.”
Ya qara da cewa ”Bamu nemi taimakon Gwamnatin Tarayya da ta datse hanyoyin sadarwa ba, muna kira ga mazauna Kaduna da suyi watsi da wannan jita-jitar, su ci gaba da al’amuransu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.