Shugabannin jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida IBBUL dake Jihar Niger sun sanar da dalibai cewa an kara kudin makarantar ga dukkan dalibai.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwannatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin El Rufa’i ta ninka kudin makarantar kasu Wanda hakan ya janyo cheche kuce sosai da zanga zangar dalibai amma duk da haka gwannatin bata fasa ba.
A cewar takardar wacce Rijistran jami’ar, M.A Abdullahi ya rattafa hannu, dalibai zasu fara biyan kudi har naira Dubu dari biyu (N200,000).
A karin da aka yi, sabbin dalibai yan asalin jihar Neja zasu fara biyan N129,675.00 yayinda tsaffin dalibai zasu fara biyan N67,925.00.
Dalibai kuma wadanda ba yan asalin jihar ba zasu fara biyan N200,210.00 yayinda tsaffin zasu fara biyan N117,325.00
“Muna sanar ga daukacin jama’a, musamman iyaye, sabbi da tsaffin daliban jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai, cewa shugabannin makarantar a zamansu na 50 ranar Talata, 1 ga Yuni, 2021, sun amince da kara kudin dukkan dalibai daga sabuwar Shekarar 2020/2021.
Saboda haka, dukkan sabbi da tsaffin dalibai su fara rijista ranar 16 ga Agusta, 2021. Duk wanda kuma bai yi da wuri ba za’a ci shi tara.