Iyayen daliban da aka yi garkuwa da su na makarantar sakandire ta Bethel Baptist dake jihar kaduna, sun koka cikin tsananin baqin ciki kasancewar sauran daliban 80 har yanzu suna hannun ýan garkuwa da mutane.
In zamu tuna, ýan garkuwar sun kwashi yaran ne ranar litinin 5 ga watan juli na shekarar 2021, inda suka dauki dalibai 161.
A cikinsu dalibai 41 ne suka kubuta inda guda biyu suka tsere, daya an sako saboda rashin lafiya sai kuma guda 38 a bisa yarjejeniyar fansa.
Fiye da makarantu biyar ne a kaduna suka samu harin ýan garkuwa, sanadiyyar haka dalibai shida suka rasa rayukansu da yawa kuma suka raunata, kamar yadda gwamnatin kaduna ta tabbatar da cewar bazatayi sulhu da ýan ta’adda ba.
Hakan yasa gwamnatin kaduna ta canjawa ýan bautar qasa waje ta kuma rufe makarantu13 da suke cikin hadarin farmakin ýan bindiga.
DAILY EPISODE ta tattara cewar, adadin dalibai 80 ne suke hannun ýan garkuwa, inda kimanin kudi naira miliyan 60 aka kashe don kubutar da wasu daga cikin daliban.
Shugaban jiha na qungiyar Christian Association of Nigeria (CAN), Rev. John Joseph Hayab, a wata hirar shi da reuters ya bayyana cewa ýan garkuwar na neman kudi a qalla miliyan daya akan kowane dalibi inda ya hada jimillar kudi naira miliyan 80 a matsayin kudin fansar su.
Iyayen sun bayyana cewar su kadai suke jin zafi na rashin yaransu a tare da su.
Wani daga cikin iyayen ya bayyana irin matsanancin halin da suke ciki, inda yake cewa “Na saida gonaki da wasu muhimman kadarorinmu, har yayan yaron sae da ya sadaukar da kudin karatunsa don dai yaga qaninsa ya kubuta”.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER