Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta kaddamar da shirin N-Power Batch C kashi na farko, mutane 510,000 a fadin kasar nan ne za su amfana.
A yayin kaddamarwar, Sadiya Umar Farouq, ministar kula da ayyukan jin kai, kula da annoba da ci gaban zamantakewa, a jawabinta ta taya wadanda suka samu nasarar cin gajiyar shirin murna.
Ministar ta ce an raba N-Power Batch C zuwa kashi biyu; kashin farko mutane 510,000, inda kashi na biyu mutane 490,000.
Ta qara da cewa, a karkashin Batch C kashi na farko an zabi mutane 450,000 masu matakin karatu na digiri, yayin da mutane 60,000 su ka kasance a karkashin bangaren wadanda ba su kammala karatun su ba. Masu matakin digiri, za a dinga biyansu Naira 30,000 duk wata har tsawon shekara daya, wadanda basu kammala karatu ba za su sami Naira 10,000 duk wata har tsawon watanni Tara.