Ýan bindiga sun shiga qauyen Dan Kumeji da ke karamar hukumar kankara jihar Katsina, da misalin qarfe 11 na daren Alhamis.
Sun shiga qauyen ne suna harbi kan me uwa da wabi inda suka kashe mutane 9 suka raunata wasu da dama suka kuma yi garkuwa da mutane 7, an samu damar kai wadanda aka raunata asibiti bayan an gama farmakin.
Mazauna yankin sun yi kukan cewa sun sanar da jami’an tsaro a yayin farmakin amma basu zo ba har ýan ta’addan suka ci nasarar qudurinsu.
Har yanzu dai bamu ji komai daga bakin ýan sandan ba.
Anyi qiyasin manoma 600 ne suka qauracewa gonakin su sakamakon fargabar garkuwa ko harin ýan bindiga, duk da ana cikin yanayi na tsadar kayan masarufin kuwa.
Idan bamu manta ba a kwanakin baya Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bada izinin kowa ya dauki makami don kare kanshi. Inda kuma Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya bada izinin harbi nan take ga duk wanda aka gani da makami ba bisa doka ba.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER