Ýan bindigar da sukayi garkuwa da daliban Salihu Tanko Islamiyya, Tegina da ke jihar Neja sun sako su a yammacin ranar Alhamis.
In ba mu manta ba sun yi garkuwa da dalibai 136 ne ranar Lahadi 30 ga watan Mayu, a Tegina qaramar hukumar Rafi da ke Neja.
Sha shida daga cikin daliban sun samu kubuta inda guda shida suka rasa rayukansu sanadiyyar cututtuka da dama a lokacin da suke tsare.
Daily Episode ta tattaro cewa daliban an sake su ne a qauyen Kampany Doka da ke qaramar hukumar Birnin Gwari, Jihar Kaduna, a bisa yarjejeniyar kudin fansa.
Iyayen yaran sun hada kimanin kudi naira miliyan 50 inda ýan bindigar suka qi amincewa su sake yaran akan suna buqtar kudi naira miliyan 200.
A haka dai iyaye, ýan uwa, abokan arziqi da ma wasu suka qara tattara kudi kimanin naira miliyan 30, amma du da haka haqansu bai cimma ruwa ba domin ýan bindigar sun riqe wanda ya kai kudin akan sai an ciko naira miliyan 4 da dubu dari shida.
Bincike ya bayyana cewa an biya qarin naira miliyan 20, inda mazaunin garin wanda ya shaidawa Daily Episode cewa a yayin karbo yaran ya ga sababbin babura qirar Honda ACB guda shida wanda a qalla kowanne daya zai kai naira 650,00.
Daga nan an dauki yaran zuwa mina babban birnin Neja, inda likitoci suke duba su kafin daga bisani a hada su da iyayensu.