Kimanin mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon bullar cutar amai da gudawa a jihar katsina.
Kwamishinan lafiya na jihar ne Yakubu Danja ya tabbatar da hakan yayin da yake tattaunawa da shugabannin kungiyar likitoci ta kasa NMA a jihar.
Kwamishinan yace ” sama da mutum 1400 ne suka kamu da cutar tun bayan da ta bulla a jihar zuwa yanzu”.
Ya qara da yin kira ga jama’a da su kula da tsaftar muhallinsu da tsaftace abin ci da abin shan su.
Sanadiyyar samun barakar cutar da akayi ta bulla jihohin Kano, Zamfara, Jigawa da Sokoto, inda kuma ake samun asarar rayuka da dama.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER