Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar bazata yi sulhu da masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan bindiga ba.
Karamin ministan ilimi Chukwu Emeka Nwajiubu ne ya sanar da manema labarai hakan.
Ministan ya bayyana cewa gwamnati taqi yin sulhu da masu aikata ta’addanci da tada hankulan mutane ne duba da cewa biyansu kudin fansar na qara masu qarfi ta hanyar taimaka masu wajen mallakar makamai.
Nwajiubu yace, gwamnatin tarayya na daukar matakan samarwa da dukkanin al’ummar qasar nan tsaro, ta hanyar yaqi da ýan bindiga musanman ma a yankin arewa maso gabas.