In baku manta ba a baya ana neman matsayane tsakanin gwamnatin tarayya da qungiyar likitoci masu neman qwarewa (NARD). Gwamnatin Tarayya Ta Gaza Cimma Matsaya Da Likitoci Masu Neman Qwarewa
Rashin cimma wannan matsaya yasa gwamnatin tarayya tace, bazata ci gaba da biyan maaikatan kungiyar likitoci masu neman qwarewa albashiba.
Ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan yayin taron ministoci na maka-mako.
Yace, an yanke hukuncinne saboda hakan ya zama wajibi domin kuwa yajin aikin nasu bashi da makama ba shi da tushe.
Dr. Ehanire yace, kungiyar kwadago ta duniya ta amince da irin wannan mataki na rashin biyan ma’aikata albashi matuqar ba suyi aikin su ba.
Ministan ya qara da cewa, yanzu a halin da ake ciki gwamnati ta yi qarar kungiyar likitoci masu neman kwarewa a gaban kotun ma’aikata, kan cewa ba dalilin da zai sa gwamnati ta biya su albashi alhalin ba sa aiki a lokacin.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER