A wasu bayanai da muka samu rundunar jami’an tsaro a jamhuriyar Nijar sun kama wasu da ake zargin taimaka wa ƴan Bindiga a garin Ɗan Issa a jihar maradi dake jamhuriyar Nijar.
Rundunar tsaron a Ɗan Issa ta cafke mutane 17 da ake zargi da taimaka wa ƴan bindiga da bayanai da kayan buƙata – irin su abinci da makamai, kazalika kuma a hannun su an samu bindigogi, harsasai, da kuma dabbobi da ake kyautata zaton an kwashe daga hare-haren da ake fama da su a yankin.
Kuma hukumomin sun ce suna da alaka da manyan ‘yan ta’addan Najeriya, wasu ma na zargin cewa waɗanda aka kama ɗin basu rasa nasaba da ɓarayin da akayi zaman sulhu dasu a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Bisa ga wasu bayanan an bayyana yadda waɗannan mutanen suke kawo dabbobi a kasuwannin yankin na Ɗan Issa suke kuma saida su a farashin da ya kasa ga yadda ake saidawa a kasuwa lamarin da yasa aka ɗora ayar tambaya akan su.