Gwamnatin jihar Kano ta nuna rashin goyon bayanta qarara kan kirayen da wasu bangarori na kasar nan ke yi na halasta ta’ammali da tabar wiwi.
Gwamnan jihar Kano Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewar al’ummar sa basa buqatar hakan, kuma ba zai taba amincewa da hakan ba, tare da gargadin kar wanda ya tunkare shi da makamanciyar maganar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da shugaban hukumar NDLEA na kasa, janar Buba Marwa Mairitaya, ya kai masa ziyara.