Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar Manyan malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan film, mawaka da sauran daukacin al’ummar musulmi sun yi tururuwa wurin halartar jana’izar mahaifiyar Aminu Ala, shahararren mawakin nan da misalin karfe 9:06 na safiyar jiya a gidansa dake unguwar Maidile.
Kammala jana’izar ke da wuya aka tattara zuwa kaita makwancinta dake makabartar tarauni. Bayan kammala hakan ne mujallar fim ta tattauna da Ala don jin ta bakinsa inda yace:
“Dukkan mai rai mamacine kuma yana jiran ranar mutuwarsa don haka ta koma ga mahaliccinta. Muna mika godiyarmu ga ubangiji mahalicci da ya rabamu da duka iyayenmu lafiya, da mahaifina Sharif Adamu Maidoki da Mahaifiyata Hajiya Bilkisu Adamu.
Mun zauna lafiya da ita cikin so da kauna da amana kuma Allah ya rabamu lafiya, tana tsananin yabona da ‘yan uwana kuma duk ‘yan uwanta suna alfahari da ita.
Mahaifiyata mai zumunci ce don ko kwana biyu da suka gabata sai da ta kai ziyara taje duba mara lafiya a asibiti, wanda hakan yayi sanadiyyar rikicewar jikinta.Tayi fama da hawan jini na fiye da shekaru arba’in kuma mai kula da kiyaye dokokin asibiti ce.
Ala ya mika sakon godiyarsa ga duk wadanda suka halarci jana’izar da ma wadanda basu samu dama ba. Inda yace: Hakika masoya sun nuna min soyayya da halacci kuma hakan ya nuna ana zaune lafiya ne musamman abokan sana’a da iyaye.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER