Riqaqqun ýan ta’addan da aka fi sani da Ýan bindiga, wadanda suka yi kaurin suna wajen satar shanu, garkuwa da kisan mutane a yankin Arewacin Najeriya, sun yi garkuwa da mutane kimanin 970, inda suka kashe mutane a ‘kalla 1972 a fadin jihar Kaduna a shekarar da ta gabata.
Kwamishinan kula da tsaro da ala’muran cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da hakan a bayaninsa a wani taro da Nigerian Institute of Public Relation (NIPR) ta shirya a ranar Asabar din da ta gabata.
Kwamishinan wanda ya wakilci gwamnan jihar Kaduna a taron ya bayyana yadda karara sakacin gwamnatin da ta shude wajen kula da masu satar shanu ya haifar da halin da ake ciki yanzu a Arewacin Najeriya.
A cewarsa ýan bindiga qungiyar wasu bata gari ce da take wakiltar ta’addanci ba ta shafi yare ko addini ba, ba kamar a baya ba da aka ta’allaqa laifukan ga fulani makiyaya ba, Gwamnan ya zargi bata garin da suke kaiwa fulani hari da sunan fansar wani aikin ta’addanci da aka yi masu ko kawai saboda qabilanci wanda hakan shi ya tunzura fulanin har suka yawaita wajen aikata laifuka kuma mafi yawan da abin yake shafa.
Ya qara da cewa yawaitar makamai da qwayoyi sun qara tabarbarewar lamarin gyaran tsaro. Amma du da haka gwamnatin Kaduna tayi iya bakin qoqarin ta wajen qwace muggan makamai da dama tun daga farkon shekara har zuwa yanzu.
Cikin makaman da aka samu nasarar karba sun hada da; bindiga me tashin bom RPG guda daya, AK 47 guda 44, AK 49 guda 1, Barika pistol guda 1 da kuma bulet guda 4,4884.
Ya qara jaddada cewar tun shekarar 2015 gwamnatin Kaduna ta tsaya akan cewar bazata yi sulhu da ýan bindiga ba ko biyan kudin fansa ga masu garkuwa saboda hakan yana qara sa mutanene cikin hatsari da kuma qarfafa ýan ta’addan. A sabili da haka bekamata ace dan ta’adda yana cin ribar laifukan da yake aikatawaba yakamata ne ya fuskanci hukunci da fushin doka.