">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Thursday, August 14, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wadanda Suka Kashe Tsohon Kwamishina a Katsina

by Humaira Muhammad
July 30, 2025
in Labarai
0
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wadanda Suka Kashe Tsohon Kwamishina a Katsina
Share on FacebookShare on Twitter
">

Babbar Kotun Jihar Katsina mai lamba 9, karkashin jagorancin Mai Shari’a I.I. Mashi, ta yanke hukuncin kisa ga mutum biyu da aka samu da laifi a kisan gilla da aka yi wa tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Katsina, marigayi Honourable Rabe Nasir, a shekarar 2021.

Kotun ta tabbatar da cewa Shamsu Lawal tsohon mai gadin marigayin da Tasi’u Rabi’u wanda ke aikin girki a gidan mamacin sun bai wa Rabe Nasir abinci mai guba wanda ya kashe masa jiki don ya gaza komai sai yanda akai da shi, wanda ya janyo mutuwarsa, bayan an samu damar caccaka masa wuƙa. Hakan ya tabbata ne bisa binciken da asibiti ta gudanar, wanda ya nuna akwai guba a jikin mamacin, da kuma hujjojin binciken ‘yan sanda.

Baya ga hukuncin kisa da aka yanke wa mutum biyun, kotun ta kuma yanke hukuncin dauri na shekaru biyar a gidan yari ga wani tsohon mai gadi, Sani Sa’adu, bayan da aka same shi da laifin boye gaskiya game da lamarin kisan.

A gefe guda, kotun ta sallami wata yarinya mai suna Gift Bako, wadda aka kasa gabatar da hujjoji masu gamsarwa da ke da nasaba da laifin. Lauyanta, Barista Shedrack, ya yaba da hukuncin kotun, yana mai cewa hukuncin ya tsaya kan gaskiya. Haka kuma, lauyoyin dukkan ɓangarorin sun bayyana gamsuwarsu da yadda shari’ar ta gudana da kuma hukuncin da aka yanke.

RelatedPosts

Ana Neman Tallafin Jama’a Domin Ceto Jariri da Aka Haifa da Cutar Gastroschisis a Jigawa

An buƙaci ‘yan Kano da Jigawa da ke kewayen Tiga Dam da su tashi saboda fargabar ambaliyar ruwa

Gwamnan Katsina ya naɗa Jamil Mabai a matsayin Mataimaki na Musamman

Hotuna: Rundunar Tsaro Ta Ragargaza Ƴan Ta’adda da Sansaninsu a Borno

Lauyan waɗanda aka samu da laifi, Barista Ahmad Murtala Kankia, ya roƙi kotu da ta yi sassauci a hukuncin, yana mai jaddada cewa wadanda lamarin ya shafa na da nauyin iyaye da iyali da ke dogara da su. Sai dai, lauyar masu gabatar da kara, ta nuna jin daɗinta da hukuncin, inda ta ce ya yi daidai da doka kuma an samu adalci.

Wakilan Katsina Times da suka halarci zaman kotun sun shaida cewa wadanda aka yankewa hukuncin sun shiga cikin firgici lokacin da jami’an tsaro suka shigar da su cikin mota domin wucewa da su gidan yari. Haka zalika, an hangi farin ciki da jin daɗi a fuskar ‘yan uwa da lauyoyin Gift Bako bayan kotun ta wanke ta daga zargin.

Marigayi Rabe Nasir ya rike mukamin Kwamishinan Kimiyya da Fasaha a Jihar Katsina a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari. Haka kuma, ya kasance ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Mani da Bindawa a shekarar 2003, tare da riƙe mukamin jami’in hukumar DSS a baya.

">

A bangare guda, akwai wasu mutane biyu da ke da hannu a shari’ar, da suka kai kara a Babbar Kotun Kaduna, suna neman dakatar da cigaban shari’ar a Katsina.

">

DAILY EPISODE HAUSA

Humaira Muhammad

Humaira Muhammad

Related Posts

cutar gastroschisis

Ana Neman Tallafin Jama’a Domin Ceto Jariri da Aka Haifa da Cutar Gastroschisis a Jigawa

by Abubakar Ismail kankara
July 30, 2025
0

Kasa da sa’o’i 24 da haihuwarsa, jariri mai suna Salisu Sale wanda aka haifa da cutar gastroschisis – wata larura...

ambaliya

An buƙaci ‘yan Kano da Jigawa da ke kewayen Tiga Dam da su tashi saboda fargabar ambaliyar ruwa

by Abubakar Ismail kankara
July 25, 2025
0

Biyo bayan hasashen da Hukumar Yanayi ta Ƙasa (NiMet) da Hukumar Kula da Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) suka fitar, wanda...

Jamil Mabai

Gwamnan Katsina ya naɗa Jamil Mabai a matsayin Mataimaki na Musamman

by Abubakar Ismail kankara
July 19, 2025
0

A wani mataki na ƙarfafa shugabanci da inganta hanyoyin sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar...

Hotuna: Rundunar Tsaro Ta Ragargaza Ƴan Ta’adda da Sansaninsu a Borno

by Abubakar Ismail kankara
July 7, 2025
0

A wasu hotuna da rundunar sojin Najeriya ta fitar, an nuna yadda dakarunta suka samu nasarar kashe ƴan ta’adda da...

Fursunoni

Fursunoni 58 Sun Rubuta Jarabawar NECO A Gidan Yarin Kano

by Abubakar Ismail kankara
July 7, 2025
0

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa (NCoS) reshen jihar Kano ta bayyana cewa fursunoni 58 ne suka zana...

fasahar ƙirƙirar basira

AI na Barazana Ga Ayyuka Sama da Miliyan 92 a Duniya — Farfesa Umaru Pate

by Abubakar Ismail kankara
July 7, 2025
0

Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere (FUK), Farfesa Umaru Pate, ya bayyana cewa sama da ayyuka miliyan 92 na iya salwanta...

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In