Sheikh Abduljabbar dai yayi fumfurus inda yaqi cewa komai game da sababbin zarge-zargen da aka yi masa.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da cin zarafin Annabi Muhammadu (SAW) a ranar Juma’a 16 ga watan Yuli.
An fara zaman ne a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu daura da gidan Sarkin Kano da misalin karfe 9:20 na safe, tare da gabatar da wasu sabbin tuhume-tuhume kan wanda ake zargin.
A yayin zaman ne kotu ta ba da umarnin a gudanar da gwajin lafiyar kwakwalwa da kuma kunnen Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola ne ya bayar da umarnin yayin zaman kotun ranar Alhamis, bayan amincewa da bukatar Babban Lauyan Surajo Sa’ida.
Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola ya ce likitan kwakwalwa daga Asibitin Kula da Masu Tabin Hankali da ke Dawanau a kano, sai kuma liktitan kunne daga Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano ne za su duba malamin sannan su kawo wa kotun rahoton bincikensu.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER