A yayin da jihar Zamfara tayi kaurin suna wajen masu garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci da dama da ya addabi yankin, ýan sanda na iya bakin qoqarinsu wajen kawo qarshen abun.
Rundunar ýan sandan ta jihar Zamfara sunyi babban yunquri inda suka ceto mutane 8 daga hannun ýan bindiga.
A ranar 25 ga watan Agusta ne masu garkuwar suka sace mutanen 8 a kauyen Kangon Sabuwa da ke karamar hukumar Bungudu jihar Zamfara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ýan sandan jahar, SP. Shehu Muhammed, ya tabbatar da an kubutar da mutanen cikin koshin lafiya an kuma miqa su ga iyalansu, ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin din da ta gabata.