Iskar gas a Najeriya tayi tashin gwauron zabi sanadiyyar qarin haraji na VAT da Gwamnatin tarayya ta yi da kaso 7.5.
Gwamnatin tayi karin harajin ne a makonni uku da suka gabata wanda ya janyo hauhawar farashi.
Shugaban Kamfanin na kasa Michael Umudu ya bayyana cewa karin farashin iskar gas din ya ta’allakantu ne a kan dalilai uku wanda ke kawo hauhawar farashin gas din da ake amfani da shi a Najeriya da kaso 70 cikin 100. Babban dalilin da yake janyo hawan farashin shine shigo da shi daga kasashen waje.
Shugaban ya qara da cewar domin samar da wadatacciyar iskar gas, Najeriya tana shigo da kaso 70 cikin 100 na iskar gas din da ake amfani da shi, ya sanar da hakan ne a wata zantawa da yayi da manema labarai.
Farashin iskar gas din ya tashi da kashi 100 cikin watanni 8 da suka gabata, in da ake siyan iskar gas mai nauyin kilo 12.5 akan 4000 a qarshen shekarar 2020 yanzu kuma akan 7500 a Kaduna.