Shugaban kasa Muhammadu Buhari ana sa ran zai kaddamar da shirin Jubilee Fellows, shirin zai samarwa da matasa 20,000 abin yi.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Mr. Tolu Ogunlesi, ya sanar da hakan ne a ranar Litinin.
Shirin ya samu tallafin United Nation Development Programme ne (UNDP).
Ana sa ran sanarwane idan duka tsare tsare suka kammala ranar Talata.
An tsara shirin ne domin rage talauci da rashin aikinn yi a kasar. Inda za a dauki matasan da basu wuce shekaru 30 ba.
Kimanin matasa 20,000 ne da suka kammala karatu za a dauka aiki na tsawon wata 12 a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER