Arewacin Najeriya na cikin inna-naha, duba da yadda ayyukan ýan bindiga kullum abin yake qara ta’azzara.
A Jihar Katsina wani fitaccen ‘dan ta’adda mai garkuwa da mutane mai suna Usman Idris da aka fi sani da Ruga Kachallah, ya nemi a biya shi diyyar buhunhunan hatsin sa da jami’an ‘yan sanda su ka banka wa wuta, kafin a yi sulhu da shi.
Kachallah shi ne babban gogaggen dan ta’addan da ya hana Ƙaramar Hukumar Safana zaman lafiya da kewayen ta a Jihar Katsina.
A ranar 25 Ga watan Mayu ne, jami’an tsaro suka kai wa Kachalla sumame har gidan shi, sai dai anyi rashin sa’a ba su same shi ba, inda suka cinnawa gidan wuta, su ka ƙone buhunhunan hatsi. Sannan kuma suka tafi da matan sa guda biyu.
Inda ‘yan garin saboda tsoro da fargabar abinda zai iya aikata musu yasa sukayi taron-dangi suka kashe wutar.
Wannan lamari ne fa ya fusata Kachalla, ya riƙa kama mutane, har sai da aka sakar masa matansa biyu sannan ya sake su. Kuma ya ƙara ƙaimi sosai wajen kama mutane ya na yin garkuwa da su, ana biyan sa diyya.
Sakamakon hakan ya sa Kachalla neman zaman sulhu tare da bada sharadin cewar a biya shi diyyar barnar da aka yi masa ta qona mai gida.
Sai dai kuma Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ta yi fatali da buqatarsa, inda ta bayyana cewa sau huɗu ana zaman sulhu da Ruga Kachallah amma yana karya wa.
Rahotanni sun bayyana cewa, Kachalla yana da tarin ‘yan bindigar da su ke ƙarƙashinsa, waɗanda sun fitini garuruwa da ƙauyukan yankin da garkuwa da satar shanu da dukiyoyin jama’a.
Kachallah ya tara maqudan kudade da yake sana’o’i da dama a yankin Safana.
Ya mallaki motocin haya sosai waɗanda ake yi masa jigila garuruwan yankin ana tara masa kuɗaɗe.
Wannan sana’a da Kachalla ke yi ta samar wa matasa da dama aikin yi a kewayen. Kuma su na hamdala sosai ga Kachallah, wanda hakan ya qara mai farin jini a wajen jama’ar yankin.
Mutanen karkarar Rulumbusawa, Yartsaku, Maƙera, Gimi da Chirena da ke cikin Ƙaramar Hukumar Safana a Jihar Katsina, sai sun nemi iznin Kachallah kafin su fita zuwa gonakin su.
A Arewacin Runka, gari na biyu wajen girma a Ƙaramar Hukumar Safana, can ma manoma sun miƙa wuya ga ‘Daular Kachallah’, gogarman ‘yan bindiga.
Ba kamar sauran ‘yan bindigar da ke ɓoye a cikin daji ba, shi Ruga Kachallah a cikin garin Gimi ya ke zaune da iyalin sa. Ya san kowa, kowa ya san shi.
Kwanan nan mazauna garin sun hana jami’an ‘yan sanda kama wani yaron sa, wani ɗan ta-kife, mai suna Gulbi.
An ce Kachallah na bai wa Gulbi shanun da ya sato, shi kuma ya na sayar masa.
Lokacin da mazauna garin su ka hana ‘yan sanda kama Gulbi, sun shaida wa Kwamandan Eriyar Safana, Dutsin-Ma, Ɗanmusa, Kurfi da Batsari, Aminu Umar-Daye cewa, ba za su bari a kama Gulbi ba, saboda idan aka kama shi, Kachalla cewa zai yi da haɗin bakin jama’a aka kama Gulbi, kuma a kan su zai huce haushin sa.
Haka dai Umar Daye ya haƙura ya janye ‘yan sandan.
Cikin 2016 ne Riga Kachalla ya haɗa kai da wasu fitinannun ‘yan bindiga da su ka haɗa har da Abdullahi Karki, wani tubabben ɗan bindiga a yanzu, su ka yi alƙawarin ajiye makamai a wani ƙwarya-ƙwaryan bikin karɓar tubar su a ƙarƙashin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa. An yi bikin a ƙauyen Illela, cikin Ƙaramar Hukumar Safana.
Sai dai kuma ba a daɗe da yin sulhun ba, sai dakarun Kachalla su ka koma bakin aikin kama mutane, su na yin garkuwa da su, ana biyan Kachalla kuɗaɗen fansa.
Bayan jami’an tsaro sun matsa lamba, wani dakaren Kachalla mai suna Jummah Tambai, ya kwashe iyalin sa ya koma Jihar Nassarawa, daga can kuma aka ce ya koma wani wurin da ake haƙar ma’adinai a cikin dajin Jihar Osun.
Haka shi ma mahaifin Kachalla da ke zaune a ƙauyen Sulluɓawa cikin Ƙaramar Hukumar Safana, ya yi hijira ya koma garin Banki cikin Ƙaramar Hukumar Anchau, saboda ya kasa hana ɗan sa Kachalla ci gaba da fashi, hare-hare da garkuwa da mutane.