Shugban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce harin da ‘yan bindiga suka kai Kwalejin Horas da Sojoji ta NDA Kaduna ya qara qarfafawa gwamnati da jami’an tsaro gwuiwa ne.
Shugaba Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan sojoji biyu da ýan bindigar suka kashe a ranar Litinin da tsakar dare, yana mai tabbatar da cewa sai an dauki fansar rayukansu ba zasu tafi a banzaba, cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban qasar Femi Adesina ya fitar a ranar Laraba.
Shugaba Buhari ya ce wannan harin da aka kai zai jawo hanzarta kawo ƙarshen duk wani aikin ta’addanci a qasar, ganin cewa harin na zuwa ne a lokacin da sojojin suka matsa wa ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka, kuma abin da sojoji ke yunƙurin cimmawa kenan cikin ƙanƙanin lokaci.
Sanarwar ta ƙara da cewa “maimakon hakan ya sanyaya gwiwar dakarunmu kamar yadda aka tsara, zai ƙara musu azama ne wajen kawo ƙarshen miyagu a ƙasar nan, a cewar Buhari”.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER