Hedikwatar tsaro a Najeriya sun dauki alwashin lalubo ƴan bindigar da suka kashe musu sojoji tare da sace wasu jami’an sojojin bayan wani hari da suka kai a makarantar soji ta NDA a Kaduna.
Shugaban hafsoshin sojin Najeriya Janar Lucky Irabor, ya mika sakon ta’azziya ga iyalan sojojin da aka kashe, sannan ya shaida cewa an sake inganta tsaro a makarantar da kewayenta, a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce yanzu haka an bazama a wani samamen haɗin-gwiwa domin ceto sojan da aka sace da kuma kama ƴan bindigar.
Sanarwar ta kuma shaida cewa nan gaba za a sake fito da wasu bayanai kan halin da ake ciki.