In zamu tuna, ýan garkuwar sun kwashi yaran ne ranar litinin 5 ga watan yuli na shekarar 2021, inda suka dauki dalibai 121.
A ranar dai ’yan bindiga suka yi wa makarantar sakandire ta bethel baptist da ke garin Damishi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia dirar mikiya da misalin karfe 2:00 na dare sannan suka tafi da daliban.
Jimillar adadin dalibai 41 ne suka samu kubuta daga hannun ýan bindigar a baya, 38 bisa yarjejeniyar fansa, biyu suka kubuta, sai kuma daya a kan rashin lafiya.
Ýan Bindigar sun sake sakin ɗalibai 15 daga cikin waɗanda suka yi garkuwa dasu a bisa yarjejeniyar fansa.
Shugaban jiha na qungiyar Christian Association of Nigeria (CAN), Rev. John Joseph Hayab, ya shaida cewa an saki ɗaliban ne a daren Asabar bayan an biya kuɗin fansa. Ya ce har yanzu akwai yara 65 a hannun ‘yan bindigar.
Adadin yara 53 ne suka kuɓuta a bisa yarjejeniyar fansa.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER