Ýan bindiga sun kai hari Kwalejin Koyon Aikin Gona da ke Karamar Hukumar Bakura a Jihar Zamfara, sannan sunyi nasarar sace dalibai da dama.
An kai harin ne cikin daren ranar Lahadi, inda ýan bindigar sun shiga makarantar inda suka yi musayar wuta da ýan sandan da ke gadin makarantar, har hakan yayi sanadiyyar rasa ran wani ‘dan sanda.
Ko da aka tuntubi mai magana da yawun ýan sanda, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER