Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana cewa ‘yan bindiga suna kwasar kashinsu a hannu sakamakon hare-haren da suke kai musu a maboyarsu ba kakkautawa.
Rundunar sojojin sun yi nasarar kashe ýan bindigar da dama tare da jigata su.
Rundunar sojojin ta bayyana cewa ta samu wannan nasara ne lokacin da jirgin yaki mai saukan angulu mallakar rundunar sojojin saman Najeriya ya kai samame a Jihar Neja.
Idan ba a manta ba dai, Jihar Neja tana daya daga cikin jihojin da ‘yan bindiga suka addabawa da hare-hare suke kuma cin karensu babu babbaka.
A satin da ya gabata, ýan bindiga sun tsare kauyen Tudun Fulani da ke babbar hanyar shiga garin Kontagora, inda har suka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na tsawon lokaci, kafin daga bisani su shige cikin daji.
A ranar juma’ar da ta gabata, ýan bindiga suka kaiwa Malam Abubakar Agaji Bobi hari cikin dare, sai dai basuyi nasarar daukar kowa ba, illa dai sun kwashe duk wani abu mai amfani a gidan.
Hakan ya faru ne sakamakon samun rahoto da iyalan mallam Abubakar sukayi dangane da harin ýan bindigar.
Mallam Abubakar dai ya taba fadawa hannun masu garkuwar, inda Allah ya tserar da shi, a wannan harin ma ya samu kubuta domin a lokacin baya gida.
A ranar Lahadi 8 ga watan Augusta, ‘yan bindiga suka sace kwamishinan yada labarai na jihar, Mohammed Sani Idris, inda ya samu kubuta a jiya Alhamis 12 ga watan Augusta 2021.
Adadin jimillar mutane 238 ne aka yi garkuwa da su a cikin Jihar Neja.
Zuwa yanzu dai jami’an tsaron hadin guiwa da suka hada da ‘yan sintiri suna iya bakin kokarinsu na ganin sun kawo karshen hare-haren ýan bindigar a jihar baki daya, kamar yadda Malam Muhammad Nasiru Manta, kwamandan ‘yan sintiri na jihar ya shaida.
Rundunar sintiri ta musamman wadda gwamnatin jiha ta kafa, sun samu horo ne daga rundunar ‘yan sanda ta jihar.
A karon farko, rundunar tana aiki kafada da kafada da jami’an tsaron hadin guiwa da suka hada da sojoji da ‘yan sanda wanda suke fafatawa da ‘yan ta’addan.