Gwamnatin tarayya ta kasa cimma matsaya tsakaninta da qungiyar likitoci masu neman qwarewa na qasa (NARD), domin kawo qarshen yajin aikin da suke yi.
Shugaban qungiyar Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, da yake zantawa da manema labarai yace ya zuwa yanzu babu wata matsaya da qungiyar ta cimma da gwamnatin tarayya.
Ya qara da cewa zasu cigaba da tattaunawa a yau Talata 10 ga watan Augusta don cimma matsaya.
Dr. Uyilawa yace yanzu haka kwamitin lafiya na majalisar wakilai yana gudanar da wani taro da ma’aikatar lafiya da kuma wakilan qungiyar don samar da sulhu a tsakani.
Inda ya qara da cewa gwamnati na roqonsu don komawa bakin aiki.
Comments 2