Gwamnatin Jihar Kaduna a yau Lahadi ta ce sojoji sun sami nasarar kashe rikakkun ’yan bindiga guda hudu a tsaunin Maikwandaraso a Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar.
Maikwandaraso dai wani tsauni ne dake dab da kauyen Karshi, kuma ya yi iyaka da dazukan Kawara da Malul, wadanda suka yi kaurin suna a yankin Karamar Hukumar ta Igabi, kuma nan ne aka yi ittifakin ya zama maboyar ’yan bindigar.
An kashe ’yan bindigar ne bayan wata musayar wuta tsakaninsu da sojoji, a yunkurin da jami’an tsaro ke yi na fatattakarsu.
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Ya ce wadanda aka kashe din sun hada da Alili Bandiro, Dayyabu Bala, Bala Nagwarjo da kuma Sulele Bala.
Kwamishinan ya kara da cewa an kashe wasu da dama yayin hare-haren da aka kai musu ta sama.
Sanadiyyar samun rahoton nasarar da sojojin suka yi, Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana farin cikinsa a kan haka, tare da godewa sojojin bisa namijin kokarin da suke yi wajen kawar da bata-garin.