Mai martaba Sarkin Kano mai murabus, Muhammadu Sanusi Lamido II, ya biyawa wadanda ke tsare a gidan kaso kimanin mutum 38 bashin da ake binsu, da kudin da ya kai sama da naira miliyan 22.
Daurarrun dake gidan gyaran hali na kurmawa, kimanin mutum goma sha hudu ne aka biyawa naira miliyan 14, sae wadanda ke Gwauron Dutse kimanin mutum ashirin da hudu aka biyawa tarar miliyan 7.
Da yake bayar da kudaden Mujittafah Abubakar Abba Falaki a madadin sarkin Kano murabus yace, an biya kudinne Fisabilillahi, kuma hakan wani bangarene na murnar cika shekara 60 da Muhammadu Sanusi Lamidon yayi.
An fara tantance daurarrun da suka rabauta, domin sallamarsu zuwa ga iyalansu kamar yadda mai magana da yawun gidajen yari, Musbahu Lawal Kofar Nasarawa ya tabbatar.