Rahotanni daga kasar Amurka na bayyana cewar Auren mashahurin mai kudin nan na duniya Bill Gates da matarsa Melinda French Gates ya rabu kamar yadda alkali babbar Kotun Amurka ya amince da rabuwar tasu a shari’ance.
Dama sun gabatar da takardar amincewa da rabuwar aurensu mai shekaru 27 tun 3 ga watan Mayu zuwa babbar kotu ta King County dake Washington kuma an tabbatar da rabuwar tasu a ranar Litinin.
Bill da Melinda sun jima suna yada rabuwar aurensu kuma sun amince da yadda zasu raba auren. Bayan sanar da shirin rabuwa, Bill Gates da Melinda sun tsinke igiyoyin aurensu.
Sai dai kamar yadda Reuters suka tabbatar, babu wani dogon bayani akan rabuwar auren sannan babu batun raba kudade, kadarori ko wasu dukiya dake tsakaninsu a rabuwar auren.
Rahoton kotu ya bayyana cewa babu wanda zai canja sunansa cikinsu ko kuma ya samu wani tallafi. Biyun sun dade suna taimakon jama’a ta gudauniyar Bill and Melinda Foundation.