Gwamnatin jihar Katsina ta dakatar da makiyaya kiwon shanu a sararin fadin jihar da zagayenta.
Sanarwar dakatar da kiwon ta samu sa hannun wakilin kudin katsina Alhaji Abdu Iliyasu.
Wakilin yace dokar zata fara aiki nan take, kuma an qaddamar da wakilan da zasu lura da dokar tana tafiya yadda ya kamata.
A watan da ya gabata gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ware wasu kudi kimanin naira biliyan shida, don samar da burtalai na kiwo ga makiyaya a jihar ta Katsina.